Acts 15

Majalisa a Urushalima

1Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ʼyanʼuwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga alʼada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.” 2Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana. 3Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Alʼummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ʼyanʼuwa suka yi murna ƙwarai. 4Saʼad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.

5Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Alʼummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”

6Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar. 7Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi, ya ce: “ʼYanʼuwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Alʼummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata. 8Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu. 9Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya. 10To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba? 11Aʼa! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”

12Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Alʼummai ta wurinsu. 13Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana, ya ce: “ʼYanʼuwa, ku saurare ni. 14Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Alʼummai su zama nasa. 15Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce, cewa:

16“ ‘Bayan wannan zan koma
in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe.
Kufansa zan sāke gina,
in kuma mai da shi,
17don ragowar mutane su nemi Ubangiji,
kuma duk Alʼumman da suke kira bisa sunana,
in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’
Amos 9.11, 12

18da aka sani tun zamanai.
19“Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Alʼummai waɗanda suke juyowa ga Allah. 20A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini. 21Gama Musa ya yi waʼazi a kowane birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majamiʼu kowane Asabbaci.”

Wasiƙar Majalisa zuwa ga Alʼummai Masu Bi

22Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin ʼyanʼuwa. 23Tare da su suka aika da wannan wasiƙa:

Daga manzanni da dattawa, ʼyanʼuwanku,

Zuwa ga Alʼummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya:

Gaisuwa.

24Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna ta da hankalinku ta wurin abin da suka ce. 25Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus—  26mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi. 27Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta. 28Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa: 29Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa.
Ku huta lafiya.

30Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar. 31Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa. 32Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa ʼyanʼuwa. 33Bayan suka yi ʼyan kwanaki a can, sai ʼyanʼuwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dāsu, 34 amma Sila ya yanke shawara ya dakata a can
34
This verse is empty in this translation.
35Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi waʼazin maganar Ubangiji.

Saɓani Tsakanin Bulus da Barnabas

36Bayan ʼyan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ʼyanʼuwa a duk garuruwan da muka yi waʼazin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.” 37Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su, 38amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba. 39Suka sami saɓanin raʼayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus, 40amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan ʼyanʼuwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji. 41Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.

Copyright information for HauSRK